ABNA24 : Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Ra’esi yana fadar haka ne a lokacin ganawarsa da shugaban kasar Iraqi Barham Saleh a jiya Laraba a birnin Bagdaza.
Ra’esi har’ila yau ya bukaci gwamnatin kasar Iraki ta gaggauta bincike don hukunta wadanda suke da hannu wajen kisan manya-manyan kwamandojin kasashen biyu Janar Qasim Sulaimani da kuma Mahdi Almuhandis, wadanda suka kasance jaruman yaki da kungiyar Daesh a kasashen biyu.
Janar Kasim Sulaimani dai ya na daga cikin kwamandojin sojojin kasar Iran wadanda suka taimakawa wajen kawo karshen ikon kungiyar Daesh a kasashen Siriya, Iraki da kuma Lebanon.
Amma a farkon shekarar da ta gabata gwamnatin Amurka da tashude ta kashe shi da wasu wasu abokansa na kasar Iraki a lokacinda ya isa kasar Iraki daga kasar Siriya.
342/